in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wanda ya kamu da Ebola cikin kwanaki uku a Najeriya
2014-09-12 10:27:39 cri

Mahukunta a tarayyar Najeriya sun yi watsi da rade-radin da ake yi cewa, wani 'dan kasar waje ya sauka filin jirgin saman jihar Legas dauke da alamun cutar Ebola.

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar a jiya Alhamis, ta ce, babu wani mutum ko daya da aka tabbatar yana dauke da cutar Ebola cikin kwamaki ukun da suka shude.

Game da yawan 'yan Najeriyar da aka hakikance sun harbu da cutar a baya kuwa, ma'aikatar ta lafiya ta ce, an samu jimillar mutane 19, da suka hada da 15 a jihar Legas dake kudu maso yammacin kasar, da kuma wasu mutane 4 a jihar Fatakwal dake kudu maso gabashin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, cikin wannan adadi, mutane 12 sun warke sarai, yayin da kuma 7 suka rasa rayukansu. Bugu da kari ma'aikatar lafiyar ta ce, a yanzu haka babu wani 'dan kasar, ko bako da aka kebe a jihohi biyun da a baya aka samu bullar cutar ta Ebola. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China