in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi maraba da sakin jami'an diplomasiyyar kasar Algeria
2014-09-07 16:49:37 cri
Ranar 6 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa, inda ya yi maraba da sakin jami'an diplomasiyyar kasar Algeria su biyu a ranar 30 ga watan Agusta, wadanda aka yi garkuwa da su a arewacin kasar Mali a shekarar 2012.

A cikin sanarwar, kwamitin sulhun ya kuma jajantawa gwamnatin kasar ta Algeria da iyalan mataimakin karamin jakadan kasar da wani jami'an diplomasiyya na daban wadanda suka mutu yayin da ake tsare da su.

Kwamitin sulhun ya kuma jaddada cewa, tilas ne a hukunta wadanda suka sace mutanen da kuma wadanda suka kashe wasu daga wadanda aka yi garkuwa da su. Sa'an nan ya kalubalanci gwamnatin kasar Mali da ta bi bahasin lamarin cikin hanzari, domin gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kotu.

Sanarwa ta ce, kwamitin sulhun ya tunatar da kasashen duniya muhimmancin bin dokokin kasa da kasa wajen daukar matakan yaki da 'yan ta'adda, ya kuma bukaci dukkan kasashe mambobin kwamitin da su kaucewa biyan fansa ga 'yan ta'adda da nufin sakin wadanda suke tsare lami lafiya ko ta hanyar cin gajiyar sassaucin da a kan yi ta fuskar siyasa kai tsaye ko a fakaice. Har wa yau kwamitin sulhun ya sake nanata bukatar sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su cikin gaggawa ba kuma tare da gindaya da wani sharadi ba.

A ranar 30 ga watan Agusta ne dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Algeria ta sanar da cewa, an saki jami'an diplomasiyyarta su 2 da aka yi garkuwa da su a Mali a shekarar 2012, amma ba ta ce kome ba dangane da lokaci da wurin da aka sake su. Sanarwar ta ce, Algeria ba ta biya kudin fansa ba, saboda hakan bai dace da matsayin gwamnatin Algeria na yaki da ta'adanci ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China