Cikin sakon da ya aika wa shugaban kasar Aljeriya, Mr. Xi ya nuna bacin rai game da rasuwa da jikkatar mutane sakamakon hadarin, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugaba Xi ya mika ta'aziya ga wadanda suka rasu, tare da jajantawa iyalen wadanda suka rasa rayukansu cikin wannan hadari.
Kana cikin sakon da ya aika wa shugaban kasar Faransa, Mr. Xi ya bayyana cewa, labarin rasuwar 'yan kasar Faransa da dama sakamakon hadarin jirgin saman na kasar Aljeriya mai lamba AH517 ya tayar masa da hankali sosai, kuma a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, yana nuna matukar juyayi ga iyalen wadanda suka rasa rayukansu cikin wannan hadari.
Saboda kyakkyawan zumunci da ke tsakanin al'ummar kasar Sin da jama'ar kasar Faransa, wannan ya sa yanzu haka jama'ar kasar Sin ke kasance wa tare da jama'ar kasar Faransa wajen tausaya musu kan lamarin da ya faru. (Maryam)