Sellal ya bayyana hakan ne ga wani taron manema labarai a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa babu wata shaida dake alakanta hadarin da harin mayakan sa kai dake Arewacin Mali, koda yake dai binciken da za a yi daga na'urorin nadar bayanan jirgin, za su fayyace ko akwai kuskure daga matukin jirgin.
Jirgin fasinjan dai wanda ke dauke da fasinjoji 'yan kasashe 14, ya fadi ne a garin Gossi dake Arewacin Mali, a kan hanyarsa ta zuwa birnin Aljiyas daga Ouagadougoun kasar Burkina Faso.
Tuni dai dakarun sojin Faransa da na MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya a Mali, su dauki akwatinan adana bayanan jirgin domin gudanar da bincike. (Saminu)