in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Aljeriya ta kara aikewa da dakaru zuwa lardin Ghardai
2014-03-17 10:31:36 cri
A jiya Lahadi ne kasar Algeriya ta kara aikewa da dakarun kwantar da tarzoma zuwa lardin Ghardai dake cikin kasar, a inda ta sha alwashin cewar, ba za ta janye sojojin ba har sai an samar da zaman lafia.

A yayin da yake magana da manema labarai a garin Ghardaia, kilomita dari shidda daga kudancin Algiers ministan cikin gida na Algiers Tayeb Belaiz ya ce hukumomin kasar da firayin ministan kasar mai rikon gado, Youcef Yousfi sun amince a kara bude binciken da zai gano asalin dalilan dake haddasa arangama tsakanin al'ummar Larabawa na Chamba da kuma Mozambite Berbers, musulmai masu bin darikar Ibadi.

Ministan cikin gidan ya ce shugaban kasar mai rikon gado, ya yi alkawarin gabatar da duk wadanda ke da hannu a cikin rikicin ga hukuma.

Shi dai rikicin da ake yi ya yi watanni ukku yana girgiza garin Ghardaia, a inda kuma ya haddasa rasuwar fiye da mutane 13, ukku daga cikin wadanda aka kashen an kashe su ne ranar Asabar din da ta shige.

A ranar Asabar din rikicin ya sa firayin ministan Kasar ya garzaya garin na Ghardaia a kokarin da gwamnatin kasar ke yi na murkushe tashin hankali da ke karuwa a birnin dake cikin Hamada.

Arangamar tsakanin kabilar Mozabite Berbers da Larabawa ta dauko asali ne tun a watan Disambar shekarar bara a sassa dabam-dabam na birnin da kuma wasu wurare dake kusa. Bayan da aka yi makonni ana gwabzawa sai yarjejeniyar da gwamnati da dattawan kasar wacce dama tana da rauni ta wargaje. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China