in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Boutefilka na Aljeriya ya yi rantsuwar kama aiki
2014-04-28 20:23:13 cri
A yau Litinin ne aka rantsar da shugaba Abdelaziz Bouteflika a karo na hudu a matsayin shugaban kasar Aljeriya kamar yadda doka ta 75 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

An rantsar da shugaban ne a fadar shugaban kasar da ke Algiers,babban birnin kasar. Wannan shi ne mataki na karshe na tsarin zaben kasar,kafin ya zama shugaban kasar a hukumance.

Tun da farko sai da shugaban ya duba faretin ban girma da sojojin kasar suka shirya masa, kana daga bisa ni manyan kusoshin kasar suka yi masa maraba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China