in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya na fatan maye gurbin Libiya a karbar bakuncin gasar CAF
2014-08-03 15:47:17 cri
Hukumar kwallon kafar kasar Aljeriya, ta bayyana aniyar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka dake tafe a shekarar 2017, idan har kasar Libiya ta janye daga karbar bakuncin gasar bisa dalilai na tsaro.

Shugaban hukumar ta FAF Mohammed Raouraoua ne dai ya bayyanawa manema labarai hakan ya yin wani taron manema labarai, ya kuma ce ya riga ya mika wannan shawara ga takwarar hukumar sa ta kasar Libiya domin nazartar ta.

Tuni dai hukumar ta FAF ta mika bukatar ta, ta karbar bakuncin gasar cin kofin na Afirka na shekarar 2019, tare da kasashen Cote d'Ivoire, da Kamaru, da Janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Zambia da kuma kasar Guinea.

Raouraoua ya kara da cewa daukacin kasashen da suka mika bukata ta su, ta karbar bakuncin wannan gasa a shekarun 2019 da 2021, ga hukumar gudanarwar kwallon kafar Afirka ta CAF, za su halarci tantancewa ran 19 ga watan Satumbar dake tafe. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China