A wannan rana, shugaba Hollande ya yi taron gaggawa karo na biyu tare da firaminista Manuel Valls, da ministan harkokin waje, da ministan tsaron kasa, da ministan harkokin cikin gida, da ministan sufuri da sauran manyan Jami'an gwamnatin sa a fadar Elysee, domin yin nazari kan sakwannin da Faransa ta samu dangane da bacewar jirgin saman Algeria, da yin shawarwari kan yadda za a gudanar da binciken sababin faduwar jirgin.
Bayan taron, shugaba Hollande ya bayyana cewa, an riga an samu akwatin nadar bayanai, tare da isar da shi zuwa birnin Gao a arewacin Mali, domin kara yin nazari kan dalilin bacewa da faduwar jirgin, kuma Faransa na fatan samun hakikanin dalilin da ya haddasa hadarin jirgin saman, ko domin yanayi ko domin sauran dalilai tunda komai na iya yiwuwa.
Bayan haka, shugaba Hollande ya kara da cewa, a wannan rana rundunar sojan Faransa ta riga ta jibge ma'aikatan ceto a wurin hadarin, domin gudanar da aikin bincike kan wannan batu. Jirgin saman da ya fadi ya na dauke da mutanen 116 cikin su akwai Faransawa 51.
Daga bisani a cikin jawabinsa, Hollande ya mika ta'aziya ga duk iyalan wadanda suka mutu a wannan hadarin jirgin saman.(Fatima)