Labarin ya tsamo maganar wani jami'in cibiyar raya sabbin makamashi ta kasar na cewa, wadannan tasoshin samar da wutar lantarki ta hasken rana za a gina su ne a tsakiya da kudancin kasar, kuma za a fara amfani da su kafin karshen shekarar da muke ciki. Wannan jami'in ya kuma jaddada cewa, shekarar 2014 shekara ce mai ma'ana ga kasar Algeria wajen yin amfani da sabbin makamashi, ganin yadda kasar ta zartas da jerin dokoki wajen goyon bayan aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana da iska. Bugu da kari, jami'in ya yi hasashen cewa, za a kara samun saurin ci gaba wajen amfani da sabbin makamashi a kasar a cikin shekaru da dama masu zuwa.
Ban da wannan kuma, kasar za ta dauki matakai domin kara kwarin gwiwa kan aikin zuba jari ga sabbin makamashi da kuma ci gabansa. An ce, kafin shekarar 2030, kasar Algeria za ta zuba jari dala biliyan 60 a wannan fanni, a kokarin biyan bukatun da yawansu ya kai kashi 40 cikin dari wajen samar da wutar lantarki ga dukkan kasar. (Zainab)