Kamfanin dillancin labaru na gwamnatin Algeria ya ba da labarin cewa, jirgin saman fasinja na Algeria ya fada a garin Gossi dake arewa maso gabashin kasar Mali. An gano tarkacen jiragen saman a sassafen ranar 25 ga wata. Bayan haka, a wannan rana ministan harkokin waje na Faransa, Laurent Fabius ya tabbatar da cewa, babu wanda ya tsira a cikin wannan jirgin saman. Fabius ya ce, bayan hadarin jirgin saman a Mali, masu aikin ceto na Faransa sun riga sun isa wurin hadarin domin fara aikin ceto da bincike. A tsakiyar ranar 25 ga wata, gidan talibijin Faransa ya gabatar da wani bidiyon, dake nuna tarkacen jiragen saman a cikin hamadar sahara.
Dadin dadawa, shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika ya sanar da shiga zaman makoki har kwanaki uku a duk fadin kasar, domin nuna juyayi ga wadanda suka mutu a hadarin. Haka ma Burkina -Faso an yi zaman makoki na tsawon kwanaki biyu daga ranar 25 ga wata, domin nuna ta'aziya ga 'yan kasar da suka mutu a hadarin jirgin saman Algeria a ranar 24 ga wata.(Fatima)