in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta tuntubi kasar Faransa game da jigilar gawawakin mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin jirgin samanta
2014-07-28 11:04:25 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Algeria suka bayar a ranar 27 ga wata, an ce ma'aikatar harkokin wajen kasar ta riga ta tuntubi kasar Faransa game da batun jigilar gawawakin mutanen da suka mutu, sakamakon hadarin jirgin saman kasarta da ya yi hadari a makon da ya gabata.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Algeria dai ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke cewa ministan harkokin wajen kasar Ramtane Lamamra, ya tuntubi takwaransa na kasar Faransa Laurent Fabius, yana kuma fatan kasar Faransa za ta yi bayani game da maganar da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi kan batun.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Faransa suka bayar dai an ce, bayan ganawar da ya yi da iyalan 'yan asalin Faransa da suka rasu sakamakon faduwar jirgin saman Aljeriyan a ranar Asabar, shugaba Hollande ya bayyana cewa, za a mika dukkan gawawakin mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin zuwa kasar Faransa domin yin bincike. Ko da yake bisa tsarin addinin kasar Aljeriyan, kamata ya yi a kai gawawakin mutanen zuwa garuruwansu domin binne su cikin hanzari.

A ranar Asabar din ne dai kuma firaministan kasar Aljeriya Abdelmalek Sellal ya bayyana cewa, kasashen Aljeriya, da Mali, da Burkina Faso da Faransa, da kamfanin kera jirgin saman na kasar Amurka, da kuma wani kamfanin kasar Sifaniya inda aka yiwo hayar jirgin, za su hada kansu wajen binciken musabbabin aukuwar hadarin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China