Shugaban rukunin sojojin injiniyoyin Sin da aka tura zuwa Mali a karon farko, Li Kaihua ya gaya wa wakilinmu cewa, wurin da jirgin saman Algeria ya fada, wato garin Gossi, yana da tazarar kilomita 60 daga birnin Gao, wurin da sansanin rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta Sin yake. Wurin ya kasance cikin yankin hamada ne, inda ake samun mazauna kadan. Kana hanyoyi sun lalace sosai a wannan yanki. A sabili da haka, akwai babban cikas wajen gudanar da aikin ceto da bincike kan hadarin.
Bisa umurnin kungiyar aikin ceton jirgin saman Algeria da ya yi hadari da tawagar daidaita rikicin Mali ta MDD, rukunin sojojin injiniyoyi na rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta Sin a Mali zai dauki nauyin dake bisa wuyansa na jigilar gawawwakin fasinjojin da suka mutu tare da rundunar sojan Faransa dake Mali.(Fatima)