in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana nazari kan bayanan da aka samu a akwatunan nadar bayanai na jirgin saman Aljeriya da ya fadi
2014-07-29 15:23:20 cri

A safiyar ranar litinin 28 ga wata, aka dauki akwatuna biyu da ke dauke da bayanai na jirgin saman Aljeriya mai lambar AH5017 da ya fadi, daga Bamako babban birnin kasar Mali zuwa filin jiragen sama na Charles-de-Gaulle na birnin Paris. Bisa labarin da muka samu, an ce, tuni akwatunan da isarsu Paris, aka kai su a hukumar binciken hadarorin jiragen sama ta Faransa, inda kwararru 6 suke nazari a kai.

A daren wannan rana hukumar ta sanar da cewa, ta riga ta samu bayanai daga akwati daya, sai dai dayan kuma ana kokarin samun bayanai daga cikinsa sakamakon lalacewarsa. Bugu da kari, sakataren gwamantin kasar Faransa da ke kula da sufuri, harkokin teku, da sha'anin su Mista Frederic Cuvillier ya bayyana cewa, za a dauki makwanni da dama wajen samun bayanai da yin nazarinsu.

Game da dalilan faduwar jirgin, ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce, yanzu lokaci bai yi ba da a tabbatar da dalilan faduwar jirgin, sai dai tabbas akwai mumunnan yanayi a daren da jirgin ya tashi. Haka zakila, sabbin bayanai sun nuna cewa, matukan jirgin sun taba bukatar canza hanya, daga nan ne kuma jirgin ya bace. Ita ma gwamnatin kasar Mali ta sanar da kaddamar da bincike bisa doka kan faduwar jirgin a wannan rana. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China