Gwamnatin kasar DRC-Congo ta bayyana burinta na kokarin dakile yaduwar cutar Ebola a cikin tsawon kwanaki 45 a yankin gundumar Equateur dake arewacin kasar.
DRC-Congo da abokan huldarta sun dauki wani babban mataki, wato na samun karfin dakile igiyar yaduwar cutar a wani wa'adin kwanaki 45, in ji ministan kiwon lafiyar DRC-Congo, Felix Kabange, a cikin wata sanarwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO). (Maman Ada)