Wasu manyan jami'an MDD sun ce, duk da cewar akwai gagarumin kalubale na matsalar kazantar yaduwar cutar Ebola a Afrika ta yamma, akwai kyakkyawon fatan cewar, za'a iya dakilar da cutar ta Ebola mai saurin kisan bil'adama.
Kusoshin MDD sun hada da Jan Eliasson, mataimakin babban sakatare na MDD, da kuma Dr. Margaret Chan, shugabar hukumar lafiya ta duniya WHO, da kuma Dr. David Nabarro, shugaban MDD a bangaren tunkarar cutar ta Ebola.
Manyan jami'an MDD sun ce, yaduwar cutar ba wai kawai matsalar kiwon lafiya ba ce, domin ta zamanto matsala dake barazana ga ci gaban kasashe, da kuma kawo cikas ga kokarin samar da taimakon agaji, da kuma yin barazana ga lamarin tsaro.
Kusoshin na MDD sun ce, MDD ta hada kawunan dukanin kungiyoyinta domin yaki da cutar, to amma sun ce, dole ne su ma kasashe da abin ya shafa sau hada kai da MDD domin kar lokaci ya kure a wajen yaki da ake yi da cutar. (Suwaiba)