Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta ce, a ranar 8 ga watan Satumba za ta zamanto mai masabkin bakin taron gaggawar majalisar zartaswa kungiyar ta AU a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Wata sanarwa daga kungiyar, ta ce, an shirya taron ne, domin samar da matsaya guda ta tunkarar cutar Ebola, tare da tantance matakan da suka dace da za su taimaka wa nahiyar Afrika murkushe annobar Ebola mai saurin kisan jama'a.
Sanarwar ta ce, taron gaggawar ya zama tilas saboda bukatar dake akwai na kowa da kowa ya fahimci ainihin wannan cutar ta Ebola, da kuma halin da ake ciki a game da matakan da ake dauka na tunkarar cutar, daga nan kuma taron zai samar da hanyoyi yakar cutar na bai daya, musamman idan aka yi la'akari da yadda cutar take yin tasiri ga harkokin jin dadin rayuwa da na siyasa da na tattalin arzikin jama'a.
Sanarwar ta ce, kasashe da dama na Afrika da suka hada da Nigeria, Botswana, Malawi, Gambia, jamhuriyar damokradiyyar Congo, da Afrika ta Kudu sun tura da gudumuwar agajin kudade da ma'aikatan lafiya da cibiyoyin bayar da magani, ga kasashen da cutar ta Ebola ta yi kamari, hakan wani karin taimako ne ga kokarin da AU ke yi tare da sauran kasashen waje wajen murkushe cutar ta Ebola. (Suwaiba)