Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya na kasar Dan Nwomeh ya bayyana ma manema labarai cewa ya zuwa yanzu duk wadanda aka kebe don masu bincike bisa zargin kamuwa da cutar an samu basu da shi sannan ana iyakacin kokarin ganin an dakile wannan annoba ta kowane fanni.
Mr Dan daga nan sai yayi kira ga al'umma da su yi watsi da jita jitar da ake watsawa na cewa wai cutar ta Ebola ta barke a Abuja.
A makon da ya gabata ne dai kasar ta sanar da cewa ta kusan zama kasa da bata da sauran masu dauke da wannan cuta,kamar yadda ministan kiwon lafiyar ta Onyebuchi Chukwu ya ce hakan zai tabbata bayan an gama binciken wassu sabbin wadanda ake zargin suna dauke da cutar tare da basu maganin rigakafi a kudancin kasar.
Minista Chukwu yayi bayanin cewa ya zuwa ranar lahadin da ya gabata, ba a samu wani sabon mai dauke da cutar ba a jihar Enugu dake kudan cin kasar inda ake fargaban ko mai yuwuwa ne wadansu mutane sun kamu da cutar ta Ebola.(Fatimah Jibril)