Kasar Najeriya ta samu mutum na bakwai da mutuwarsa ke da nasaba da cutar Ebola, in ji ministan kiwon lafiyar kasar Onyebuchi Chukwu a ranar Laraba a birnin Abuja.
Wata mata da ta kamu da cutar Ebola ta kwanta dama a wani asibitin Port Harcourt, hedkwatar jihar Rivers dake kudancin kasar.
A wannan asibitin ne kuma, Iyke Enemuo, wani ma'aikacin lafiya ya mutu da cutar Ebola, in ji ministan na Najeriya.
Cikin wannan yanayi ne, wani maras lafiya ya samu fitowa daga yankin da aka killace na Lagos a ranar Talata, bayan ya samu farfadowa daga cutar baki daya, in ji mista Chukwu.
A cewar ministan, ya zuwa yanzu mutane 18 aka tabbatar suna dauke da cutar Ebola tun farkon barkewar cutar Ebola a Najeriya, a yayin da maras lafiya biyu suke samun jinya, guda a Lagos, kana gudan a Port Harcourt. A makon da ya gabata, Najeriya ta sanar da cewa, mutumin guda ya kusan samun lafiya daga cutar Ebola. (Maman Ada)