A cikin tsarin yin rigakafin cutar Ebola, kasar Zambiya ta kafa na'urorin bincike a filayen jiragen samanta na kasa da kasa, in ji wani jami'in kasar a ranar Alhamis.
Kakakin wucin gadi na ministan kiwon lafiya na kasar Zambiya, Dennis Mulenga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kafa wadannan na'urorin bincike na da manufar gano duk wani fasinja, ko mai bulaguro dake zafin jikin da cutar Ebola ke iyar janyowa.
An kafa wata na'urar bincike da ake aiki na zafin jikin mutum a filin jiragen saman kasa da kasa na Kenneth Kaunda dake birnin Lusaka, hedkwatar kasar, kuma aikin kafa sauran na'urorin makamantan haka a filayen jiragen saman kasa da kasa zai kammala nan ba da jimawa ba, in ji mista Mulenga. (Maman Ada)