A ranar Jumma'a Ban Ki-moon ya yi taro tare da shugabanni da kwararru na hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da bankin duniya, da hukumar raya kasashe ta MDD, da dai sauran hukumomi. Mista Ban ya shaida wa manema labaru a bayan taron cewa, mahalartar taron sun yanke shawarar kafa cibiyar dakile cutar Ebola, don daidaita kokarin da sassa daban daban suke yi ta fuskar hana bazuwar cutar Ebola.
Ban da haka kuma, kwamitin kungiyar EU ya sanar a ranar Jumma'a da cewa, zai samar da tallafin kudin da yawansa ya kai kimanin Euro miliyan 140 don taimakawa kasashen Guinea, Saliyo, Laberiya, da Najeriya wajen yakar cutar Ebola. Haka kuma, an ce za a kasa kudin zuwa kashi guda 3 don kyautata fasahar aikin jinya, da horar da ma'aikatan jinya, gami da tallafawa kasashen Laberiya da Saliyo, wadanda suka fi gamuwa da matsala a fannin kasafin kudi. (Bello Wang)