Bankin raya Afirka ya kara samar da taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 60 don fuskantar cutar Ebola
Domin dakatar da yaduwar cutar Ebola a yammacin nahiyar Afirka, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta WHO ta sanar da cewa, bankin raya Afirka zai samar da karin taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 60 a yammacin nahiyar Afirka don karfafa tsarin kiwon lafiyar yankin. Ya zuwa yanzu, gaba daya bankin ya samar da dalar Amurka miliyan 210 don fuskantar cutar Ebola.
Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, bankin raya Afirka da hukumar WHO sun kulla wata yarjejeniya, inda suka sanar da cewa, za a yi amfani da kudin da bankin ya samar a fannonin da za su hada da dauka da kuma horas da ma'aikata, sayen magunguna da kayayyakin rigakafi da kuma kayayyakin agaji da ake bukata da sauransu don fuskantar cutar ta Ebola. (Maryam)