Taron a wannan karo mai shekaru biyu ya samun halartar mutane kimanin 200, ciki hadda shugabannin kasashe dake fama da cutar, wakilan wadanda suka kamu da cutar da masanan da fannoni daban-daban na duniya. Muhimman abubuwa da aka tattauna kan taro su ne, bincike da kimanta halin bunkasuwar matakan ba da jiyya da allurar, cimma matsaya daya kan wasu muhimman abubuwa yayin da za a dauki wasu matakai da tattauna kan yadda za a samun bayyanai a tsakaninsu sannan da sanarwa mahukuntan kasar bayyanai kan magunguna da za a fitar tare da sa kaimi ga kasashe masu fama da cutar da kamfanoni masu samar da magunguna da su tuntubi juna. (Amina)