in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta fitar da kudi ga asibitoci domin murkushe cutar Ebola
2014-09-04 10:58:10 cri

Ministan kiwon lafiya na kasar Ghana, Dr. Kweku Agyemang Mensah, ya bayyana cewar, gwmnnatin Ghana ta fitar da kudade fiye da dalar Amurka dubu 3,22 ga asibitoci na yankunan, sassan kasar, guda goma domin yaki da cutar Ebola, mai saurin kashe jama'a.

Ministan kasar ta Ghana, wanda ya bayyana hakan a garin Tamale, babban birnin arewacin kasar, ya ce, kudaden, za'a yi amfani da su wajen gyara wuraren killace wadanda suka kamu da cutar Ebola domin kula da jama'a, ko da cutar ta kunno kai a Ghana.

Ministan ya ce, gwamnatin kasar Ghana, ta damu matuka da bullar cutar ta Ebola, kuma hakan shi ya sa take daukar matakai na tunkarar cutar a kokarin da ake na dakile cutar mai saurin kashe bil'adama.

Ministan ya yi kira akan jama'ar kasar da jami'an kiwon lafiya da kuma 'yan kasashen waje mazauna kasar, da su hada karfi waje guda domin yaki da annobar cutar ta Ebola. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China