Hukumar samar da abinci ta MDD WFP ta ce, ta kara kaimin taimakon da take bayarwa na abinci ga kasashe 3, wadanda suka fi fama da cutar Ebola, kasashen sun kunshi Guinea, Liberia da Saliyo.
Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa 'yan jarida cewar, hukumar samar da abincin ta MDD ta kaddamar da wani shiri na gaggawa wanda zai samar da agajin abinci ga adadin mutane miliyan 1.3 a cibiyoyin ma'aikatun kiwon lafiya da kuma wuraren da aka killace wadanda ke fama da cutar ta Ebola.
Hakazalika hukumar samar da agaji ta MDD a watan da ya gabata ta ba da umurnin tura wani jirgin sama wanda zai yi zirga-zirga tsakanin manyan biranen kasashen Guinea, Liberia da Saliyo domin bayar da taimakon agaji.
Hukumar samar da abinci ta MDD ta ce, dakatar da harkokin kasuwanci da cinikayya ta abinci ya haddasa tsada da karancin abinci, kuma hakan wata barazana ce ga harkokin noma na kasar.
A makon da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta gano cewar, kasashe 6 na cikin barazana na yiwuwar yaduwar cutar Ebola, kasashen sun hada da Benin, Cote d'ivoire, Guinea-Bissau, Burkina Faso, Mali da Senegal, to amma hukumar lafiya tana yin aiki tare da kasashen domin tabbatar da cewar, sun sa ido tare da shirin tunkarar cutar ta Ebola, ko da ta kunno kai a kasashensu. (Suwaiba)