Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci bikin bude wani taron samar da horo game da yanayin aikin soji a duniya, da ma yadda za a bunkasa sabbin dabarun aikin soja da ba da jagoranci.
A jawabin sa ya yin taron wanda ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya shirya, shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari guda 4, da nufin bunkasa sabbin dabarun inganta aikin soji, yana mai cewa akwai ayyuka da dama da za a iya aiwatarwa a wannan fanni, ciki hadda baiwa wasu ka'idoji muhimmancin da ya dace, yayin da ake kara aiwatar da tsare- tsare.
Da farko dai shugaban kasar ta Sin ya ce ya wajaba a aiwatar da burin kasar, na kara karfin soji, da ba da jagoranci a fannin yadda ya kamata. Sai kuma dagewa kan 'yantar da tunani, da sauya tsoffin ra'ayoyin mutane game da aikin soja.
Abu na uku shugaba Xi ya ce ya shafi dora muhimmanci kan wasu muhimman abubuwan dake haifar da bunkasuwa a dukkan fannoni. Daga karshe kuma akwai zakulo sabbin dabaru daki-daki, domin samar da ikon dogaro da karfin kai. Ya ce ya kamata a gudanar da wannan aiki bisa halayen musamman na kasar Sin, da kuma dukufa ga inganta fifikon kasar ta Sin a wannan fanni. (Amina)