Yau Alhamis 28 ga wata, a nan Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manyan hafsoshin rundunonin sojojin kasashen Kazakhstan, Kyrgyzstan, Rasha, Tajikistan da Uzbekistan, wadanda suka halarci taron manyan hafsoshin sojan kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO.
A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na mai da hankali kan kyakkyawar rawar da kungiyar SCO take takawa wajen tabbatar da tsaro da samun bunkasuwa a yankin da kungiyar take ciki. Sin tana son hada kai da sassa daban daban wajen gudanar da taron koli na Dushanbe yadda ya kamata, aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da kulla kyakkyawar makwabtaka a tsakanin kasashe mambobin kungiyar cikin dogon lokaci, da kara azama kan ganin kungiyar ta kara taka rawa wajen tabbatar da tsaro, raya tattalin arziki da yin mu'amalar al'adu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin na bin manufar raya kasa cikin lumana, da samun bunkasuwa da wadata tare da kasashe masu makwabtaka da ita. (Tasallah)