in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi na cikin makoki sakamakon hadarin jirgin saman Taiwan
2014-07-24 10:38:14 cri

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya mika ta'aziyyarsa a sakamakon hadarin jirgin saman na Trans-Asia, Flight GE 222.

Wata sanarwa daga ofishin kula da harkokin jihar Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin SCTAO ta ce, Xi, wanda ke ziyarar aiki a Latin Amurka ya damu kwarai a sakamakon asarar rayuka da aka yi, a hadarin jirgin saman, kuma ya umurci ofishin SCTAO, da ta mika ta'aziyyarsa, ga bangarorin da abin ya shafa a Taiwan, a game da asarar rayukan da aka yi.

Sanarwar ta ofishin kula da harkokin jihar Taiwan SCTAO, ta ce, shugaban ofishin ya tuntubi hukumar kula da harkokin babban yankin kasar Sin ta jihar Taiwan, a game da abin da ya faru, kuma ya ce, babban yankin na kasar Sin, a shirye yake ya ba da duk wata guddumuwa da ake bukata. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China