in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da babban sakataren MDD
2014-08-16 16:24:17 cri

Yau Asabar 16 ga wata da safe, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da Ban Ki-moon, babban sakataren MDD a birnin Nanjing da ke gabashin kasar Sin.

A yayin ganawar, mista Xi ya ce, shekarar 2015, shekara ce ta cikon shekaru 70 da kafuwar MDD. Ya kamata kasashen duniya su yi amfani da wannan kyakkyawar dama wajen tabbatar da kundin tsarin MDD da kuma ka'idojin majalisar, da inganta yin mu'amala a tsakanin sassa daban daban, a kokarin kara azama kan bunkasuwar duniya cikin lumana. Kasar Sin kuma za ta halarci taron koli da majalisar za ta shirya a watan Satumba mai zuwa game da sauyin yanayi, a kokarin sa kaimi kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen daidaita sauyin yanayi.

Har wa yau shugaban kasar Sin ya nuna cewa, yanzu kasashen duniya na mai da hankali kan yadda ake yaki da cutar Ebola. Ya riga ya umurci hukumomin kasar da su mai da hankali kan yaduwar cutar, tare da daukar matakan da suka wajaba wajen yin rigakafin cutar.

A nasa bangaren, mista Ban ya ce, majalisar tana nan tana taimakawa kasashen Afirka da cutar take shafa wajen yaki da cutar. Ya kuma gode wa kasar Sin da ta ba da taimako da goyon baya kan lokaci, yana fatan kasashen duniya za su taimaka wa kasashen Afirka kamar yadda kasar Sin take yi a halin yanzu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China