Kasashen Sin da Mongolia sun amince su karfafa dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin su, tare da daga dangantakar bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi.
A cikin wata yarjejeniya da shugaban Sin Xi Jinping da ke ziyara a kasar ta Mongolia ya sanya wa hannu tare da takwaransa na kasar ta Mongolia Tsakhiagiin Elbegdorj, bangarorin biyu sun sake nanata kudurinsu na bunkasa dadaddiyar dangantakar abokantaka da ke tsakanin su bisa manufar samar da zaman lafiya, moriyar juna da mutunta juna.
Shugabannin sun kuma jaddada cewa, ba za su aikata duk wani abin da ya saba wa yarjejeniyar da suka sanya wa hannu ba, ko hada kai da wata kungiya da za ta ceta 'yancin cikakkaken yankunansu, tsaro da mutuncin kasashensu ba.
A nata bangare, Mongolia ta nanata cewa, gwamnatin jamhuriyar al'ummar Sin ita ce halattacciyar gwamnatin Sin, kuma Mongolia tana goyon bayan matsayin Sin game da harkokin yankunan Taiwan, Tibet da Xinjiang.
A ranar Alhamis da safe ne shugaba Xi Jinping ya isa birnin Ulan Bator don gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki 2, inda ya tattauna da takwaransa na Mongolia Elbegdorj da maraice.
A yau Jumma'a ne kuma shugaba Xi zai gana da firaminista Norov Altankhuyag, kana shugaban jihar Mongolia Hural Zandaakhuu Enkhbold. (Ibrahim)