Kamar yadda kamfanin dillancin labarun kasar Mongolia ya rawaito a ranar 22 ga wata cewa, shugaban majalisar dokokin kasar, Zandankhuu Enkhbold ya nuna godiya kan yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a kasarsa, tare da kulla yarjeniyoyi masu muhimmanci tare da bangaren Mongolia, inda ya ce takardun da aka sa hannu a kai za su taka muhimmiyar rawa wajen karfafa hadin kai da mu'ammala tsakanin kasashen 2.
A nasa bangaren, rediyon Muryar Rasha ya ba da labari a ranar 22 ga wata cewa, ziyarar da shugaba Xi ya kai a Mongolia ita ce karon farko da wani shugaban kasar Sin da ya kai a kasar cikin shekaru 11 da suka gabata. Haka zalika, shugabannin kasashen 2 sun yi amfani da wannan dama domin tattaunawa kan wasu manyan batutuwa, ta yadda za su iya gudanar da hakikanin hadin gwiwa. Wannan ziyara, a cewar Muryar Rasha, ta sheda cewa kasashen Sin da Mongolia suna kokarin kyautata huldar dake tsakaninsu da neman hadin kai a wasu sabbin fannoni. (Bello Wang)