Bugu da kari, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin girmama juna, fahimtar juna, taimakawa juna da kuma cin moriyar juna, don bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin kasar Sin da kasar Mongolia, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar yankin Asiya gaba daya.
A jawabinsa, Mr. Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasar Sin da kasar Mongolia su tsaya tsayin daka wajen taimakawa juna yadda ya kamata, duk da canje-canjen da ake fuskanta a harkokin kasa da kasa, sannan ya kamata kasashen biyu su kiyaye dangantakar dake tsakaninsu bisa fahimtar juna, da kuma tsayawa tsayin daka kan nuna goyon baya ga juna wajen kiyaye ikon mulkin kasa, tsaro da cikakken yankin kasa.
Bugu da kari, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, yankin Asiya shi ne yankin mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki, a sa'i daya kuma, yankin Asiya na fuskantar matsaloli da dama da abin ya shafa, don haka ya kamata kasashen dake yankin Asiya su inganta dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata don samun ci gaba tare, wanda ya zama wani babban aiki ga dukkanin kasashen dake yankin na Asiya. (Maryam)