Yayin da shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping yake ziyara a Latin Amurka a 'yan kwanakin baya, an sanar da kafuwar dandalin tattaunawar Sin da gamayyar Latin Amurka, wannan dai ya bayyana babban burin kasar Sin na yin kokari tare da kasashen Latin Amurka, domin ciyar da hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa zuwa gaba.
Sakamakon haka, Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta fitar da wani bayani yau Talata 29 ga wata cewar, ingantuwar hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa, za ta ba da muhimmin tasiri wajen kara sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duk duniya, da kuma samun wani tsarin duniya bisa adalci yadda ya kamata.
Bayanin ya kuma kara da cewa, kasar Sin na daga kasashe masu tasowa mafi girma. Yayin da take kokarin samun ci gaba, ko da yaushe ta kan tsaya tsayin daka kan kiyaye muradunta da na sauran kasashe masu tasowa gaba daya. Hakan ya sa kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, ayyukan hadin kai da aka daddale yayin ziyarar shugaba Xi a Latin Amurka sun shaida cewa, kasar Sin ta kara bayar da amfaninta mai muhimmanci yayin da kasashe masu tasowa ke kokarin kyautata hanyoyin cudanyarsu, da kuma habaka hadin kansu a fannonin zuba jari da harkokin kudi. (Danladi)