Bayan kammala ziyarar shugaba Xi, da ministan harkokin waje na Sin, Wang Yi ya bayyana yanayin da ake ciki a wannan ziyara inda ya ce, bisa kiran da kasar Sin ta yi an gudanar da taron shugabannin Sin da na kasashen Latin Amurka karo na farko.
A lokacin taron shugaba Xi da shugabannin kasashen Latin Amurka da na yankin Caribbean 11 sun hadu a gu daya, tare da yanke shawarar kafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a duk fannoni irin na samun moriyar juna cikin adalci da samun bunkasuwa tare tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka.
Haka kuma an yanke shawarar kafa dandalin tattaunawar Sin da Latin Amurka, wanda zai bude yunkurin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a duk fannoni, ta yadda za a kara bunkasa dangantaka tsakaninsu a nan gaba yadda ya kamata. (Fatima)