Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin sakon da ya aika wa sabon shugaban ya ce, a shirye yake ya hana kai da sabon shugaban don karfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da kasar Iraki.
Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan shirin kasar na sassanta bangarorin siyasa da sake farfado da tattalin arzikin kasar, tare da imanin cewa, al'ummar kasar Iraki za su iya magance matsalolin da suke fuskanta sannan za su maido da zaman lafiya da ci gaba cikin hanzari.
A ranar Alhamis ne 'yan majalisar dokokin kasar ta Iraki suka zabi Masoum a matsayin sabon shugaban kasar, matakin da ke nuna muhimmin ci gaban da aka samu na kafa sabuwar gwamnati a kasar. (Ibrahim)