in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yiwuwar samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila
2014-01-03 11:13:08 cri

A ranar 2 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya ce, muddin Falesdinu da Isra'ila suka yi kokari tare, za a cimma bukatar samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

A wannan rana, bayan da John Kerry ya isa Isra'ila, ya tattauna da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, amma bayan haka sun yi takaitaccen bayani game da abin da suka tattauna a kai.

A cikin bayanin Kerry, ya ce, a cikin makwanni ko watanni masu zuwa, Falesdinu da Isra'ila za su zabi wasu matakai da za a dauka, wanda ke nuna cewa za'a samar da zaman lafiya hakika ba wai a tunani ba.

A cikin nashi bayanin Firaminista Netanyahu, ya ce, cimma burin samar da zaman lafiya, yana nufi ya kamata a amince da Isra'ila a matsayin wata kasar Yahudawa, kuma dole ne shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas ya ki amincewa da ayyukan ta'addanci, ya rungumi zaman lafiya.

Bisa labarin da aka samu, an ce, domin kawar da sabanin da ke cikin shawarwari a tsakanin Falesdinu da Isra'ila, a ranar 3 Jumma'an nan, Mr Kerry zai ci gaba da tattaunawa da Netanyahu, sannan a daren wannan ranar har ila yau zuwa safiyar ranar Asabar 4 ga wata, zai gana da Abbas. Idan akwai bukata, zai ci gaba da tattaunawa da bangarorin biyu a ranar Lahadi 5 ga wata. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China