in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga zagayen farko na shawarwarin sulhu tsakanin Falesdinu da Isra'ila
2013-08-15 15:15:59 cri
Rahotannin baya bayan nan na nuna cewa, wakilan kasar Isra'ila da na al'ummar Falesdinu, sun fara gudanar da sabbin shawarwarin sulhu tsakaninsu a zagaye na farko cikin sirri a birnin Kudus a ranar 14 ga wannan wata.

Kakakin wakili mai kula da shirin shawarwarin na kasar Isra'ila, kuma ministan ma'aikatar shari'a ta kasar Tzipi Livni ce ta bayyana hakan ta wani shafin yanar gizo, da karfe 7 na maraicen ranar Laraba 14 ga wata. A cewar jami'ar, an riga an fara shawarwarin, ko da yake ba a yarjewa manema labaru shiga zauren da ake tattaunawar ba. Hakan a cewarta zai baiwa wakilan damar mai da hankali sosai kan aikin da suka sanya a baga.

Kafin dai a fara shawarwarin na wannan lokaci, ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya fayyace cewa, batutuwan da suka shafi tsaro da iyakar kasashen biyu, za su kasance a matakin farko cikin shawarwarin sulhun da za a aiwatar, matakin da muddin aka kai ga samun nasararsa, zai taimaka matuka wajen warware ragowar batutuwa cikin sauki, ciki hadda matsalar ginin matsugunnan Yahudawa.

A dai wannan rana, kasar Isra'ila ta kuma ba da wata sanarwa dake nuna cewa, za ta mikawa gwamnatin Falesdinu gawawwakin wasu Falasdinawa fiye da goma cikin 'yan kwanakin nan masu zuwa. Wannan dai mataki na zuwa ne daidai lokacin da ministan ma'aikatar kula da harkokin raya biranen kasar ta Isra'ila Uri Ariel, ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da habaka gine-ginan matsugunan Yahudawa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, tawagar wakilan kasar Falesdinu, karkashin jagorancin babban shugabanta Saeb Erekat, ta halarci shawarwarin na ranar 14 ga wata, yayin da babban wakili mai kula da shirin shawarwarin, kuma ministan shari'ar kasar Isra'ila Tzipi Livni, ya jagoranci tawagar kasarsa yayin wannan zama. Sai dai mamzon musamman na kasar Amurka Martin Indyk, wanda tun da fari aka tsara zai halarci shawarwarin a wannan zagayen bai halarci zaman ba.

A mako mai zuwa ne dai ake fatan gudanar da zagaye na biyu na zaman shawarwarin wani wuri dake yankin yammacin kogin Jordan. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China