Ko da yake jami'in ya bayyana aniyar kasar Isra'ila ta tsagaita bude wuta, amma bai yi karin bayani kan tsawon lokacin wa'adin ba.
A ranar 5 ga watan nan da karfe 8 na safe ne Palasdinu da Isra'ila suka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72, sa'an nan bangarorin biyu suka aike da manyan wakilansu zuwa birnin Alkahira na kasar Masar don tattaunawa bisa shiga tsakanin kasar Masar, da nufin kulla wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta cikin dogon lokaci.
Amma a daren jiya kakakin kungiyar Hamas ya musanta labarin tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar, inda ta ce, ba a tattauna kan batun tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta ba a yayin shawarwarin da suka yi a birnin Alkahira.
Kaza lika, kamfanin dillancin labaran Masar na MENA ya ruwaito shugaban tawagar wakilan Falesdinu Azzam al-Ahmad wanda a halin yanzu ke birnin Alkahira na cewa, ya zuwa yanzu, ba a samu labarin cewa za a tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta ba, amma akwai lokacin yin shawarwari kan wannan shiri kafin a kawo karshen wa'adin tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 da za ta kare a safiyar ranar 8 ga wata. (Maryam)