in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza
2014-07-19 21:05:36 cri
A jiya Jumma'a 18 ga wata ne aka shiga yini na goma sha daya tun bayan da sojojin Isra'ila suka fara kaddamar da hare-hare kan yankunan al'ummar Falasdinawa, bisa abin da suka kira kiyaye tsaron iyakar kasar Isra'ila, kuma yini na daya da sojojin Isra'ila suka kai harin kasa yankin Gaza.

A wannan rana, sojojin kasa na Isra'ila sun gano hanyoyin dake karkashin kasa a kalla guda ashirin dake yankin Gaza, kuma sun yi gargadi cewa, mai iyuwa ne za su ci gaba da kai hare-haren kasa a yankin. Kuma ya zuwa karfe goma na daren wannan rana, matakan sojan da Isra'ila ta dauka sun haddasa mutuwar mutane 278 a yankin Gaza.

Wani babban jami'in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa, matakan sojan da Isra'ila ta dauka za su haddasa mata illa cikin dogon lokaci bisa ga rikicin dake tsakaninta da Falesdinu.

Game da wannan rikici, gamayyar kasa da kasa na ci gaba da dukufa wajen ciyar da yunkurin tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu gaba, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ziyarci Gabas ta Tsakiya a ran 19 ga wata don kokarta aikin maido da zaman laifiya, yayin da a nasa bangare, zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi kira ga bangarorin biyu da su dakatar da bude wuta, domin kaucewa matakan da za su kara haddasa karin matsaloli ga yanayin da suke ciki a halin yanzu, yayin taron gaggawa game da rikicin Gabas ta Tsakiya a kwamitin sulhu na MDD ya kira a ran 18 ga wata.(Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China