Wani jami'in Falesdinu ya bayyana cewa, ba a samu ci gaba ba kan shawarwarin tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci da ke tsakanin Isra'ila da Falesdinu.
Bayan aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 120 a daren ranar 18 ga wata, Isra'ila da Falesdinu ba su iya cimma daidaito kan tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci ba, illa kawai sun yarda da tsawaita wa'adin yarjejeniyar zuwa daren ranar 19. Sai dai rikicin ya sake barkewa a yammacin ranar 19, lamarin da ya kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Bugu da kari, bambancin ra'ayi da ke tsakanin bangarorin biyu ya janyo cikas ga shawarwarin neman cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci, wadanda a halin yanzu, kasar Masar ke kokarin shiga tsakani a kai. (Maryam)