Mr. Wu, wanda ya bayyana hakan ga kafofin watsa labarai a birnin Tehran na kasar Iran a jiya Asabar, ya ce hare-haren da bangarorin biyu ke kaiwa juna ya janyo hasarar rayuka da dama, don haka Sin ke fatan bangarorin biyu, za su gaggauta tsagaita musayar wuta ba tare da bata lokaci ba, domin dakile kara tabarbarewar yanayin da ake ciki.
Mr. Wu ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana Allah wadai da daukar dukkanin matakan da suka iya jefa fararen hula cikin mawuyacin hali. Har wa yau Sin na ganin ba za a iya kawo karshen matsalolin da ake fsukanta ba ta hanyar musayar wuta.
A baya dai, Mr Wu ya taba gudanar da ziyarar aiki a Falesdinu da Isra'ila, a matsayin manzon musamman na kasar Sin kan batun Gabas ta Tsakiya, a yunkurin karfafa gwiwar sassan biyu wajen ganin sun kai zuciya nesa, da ma magance daukar dukkanin matakan da ka iya haddasa tabarbarewar yanayin zaman lafiyar yankin.
Ci gaban wannan rikici dai da Falesdinu ke yi da Isra'ila ya nuna matukar bukatar da ake da ita, ta komawar bangarorin biyu teburin shawara, tare da fatan za a kai ga dakatar da tashe-tashen hankula, a kuma warware takaddamar sassan biyu ta hanyar lumana. (Maryam)