in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun nasara game da dakile yaduwar Ebola a Najeriya, in ji ministan lafiyar kasar
2014-08-27 16:41:06 cri

Ministan lafiyar kasar Najeriya Onyebuchi Chukwu, ya ce ana samun karin nasara a yakin da kasar ta ke yi da yaduwar cutar Ebola. Chukwu ya ce a baya bayan nan an samu karin wasu mutane da suka warke daga cutar, tuni kuma aka sallame su daga asibiti.

A daya hannun kuma ministan lafiyar ya tabbatar da cewa duka duka mutane 13 ne suka kamu da cutar, inda 5 daga cikin su suka riga suka mutu. Sai kuma wasu mutane 7 da suka warke, yayin da ake ci gaba da kokarin jinyar wani mutum daya wanda kawo yanzu ba ya cikin wani gagarumin hadari.

Bugu da kari Onyebuchi Chukwu ya ce, akwai mutane 129, da aka kebe su aka yi musu bincike har tsawon kwanaki 21, daga bisani an tabbatar da cewa ba su kamu da cutar Ebola ba, yayin da sauran mutane 128 ana ci gaba da sanya musu ido, wadanda a cikinsu akwai mutum daya da ya nuna alamun cutar, sai dai ba a san ko ya kamu da cutar ko a'a ba tukuna. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China