140826murtala
|
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da rigakafin cutar shan inna a jihar Yobe Alhaji Muhammad Abubakar Babeh, a yayin da yake jawabi a wajen wani taro da hukumar kula da rigakafin cutar shan inna (NPI) suka shirya tare da hadin-gwiwar kungiyar 'yan jaridu (NUJ) ta kasa reshen jihar Yobe a garin Damaturu dangane da illolin cutar ta Ebola.
Shugaban kwamitin rigakafin cutar ta shan inna na jihar ya kara da cewa, 'yan jaridu na da matukar rawar takawa wajen ilmantar da al'umma. Don haka ya kamata su ci gaba da nuna jajircewa kan wannan aikinsu mai muhimmanci kuma mai lada don ganin sun ilmantar da jama'a dangane da alamomin wannan cuta ta Ebola, da kuma matakan da suka kamata a dauka don kaucewa kamuwa da ita.
A jawabinsa yayin wannan gangami na yaki da cutar Ebola, jami'in gudanarwa na hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) reshen jihar Yobe Dr. Adamu Isah ya tabo tarihin wannan cuta, inda ya gargadi jama'a da su yi hattara dangane da wannna cuta tare da yin amfani da duk wata fadakarwar da 'yan jaridu da jami'an kiwon lafiya ke bayarwa game da matakan kariya daga kamuwa da wannan cuta ta Ebola.
Dr. Adamu Isah ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Yobe da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya dangane da matakin ba sani ba sabo da suke dauka game da wannan cuta ta Ebola da ma sauran bangarori na kiwon lafiya.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.