An bude wani taron yini biyu na kwararru a fannin kiwon lafiya daga kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, domin nazartar halin da ake ciki game da yaduwar cutar Ebola.
Taron wanda tuni ya fara gudana a birnin Accran kasar Ghana, zai kuma baiwa mahalartansa damar sake nazartar matakan da ake dauka, na dakile yaduwar wannan cuta a daukacin kasashen yammacin Afirka.
A jawabinsa na bude taron, mataimakin ministan lafiyar kasar Ghana Dr. Victor Asare Bampoe, ya jaddada muhimmancin kebe wadanda suka kamu da Ebola, da matakan wayar da kan jama'a, a matsayin manyan hanyoyin dakile yaduwar cutar.
Bampoe ya kuma bukaci kwararrun dake halartar wannan taro, da su zage damtse wajen zakulo amsoshin tambayoyin game da wannan cuta, kamar batun dalilin da ya sanya ta dadewa tana yaduwa a yammacin Afirka, da batun ko hakan na da alaka da matsayin harkokin kiwon lafiya a yankin da dai sauran su.
Ko da yake ya ce, tuni hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana tasirin managarcin tsarin kiwon lafiya wajen shawo kan cututtuka masu saurin yaduwa, inda hukumar ta bayyana kasashen da ke da irin wadannan tsare-tsare a matsayin mafiya saurin shawo kan yaduwar kwayoyin cututtuka. (Saminu)