in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola za ta janyo raguwar GDP a yammacin Afrika, in ji ADB
2014-08-27 09:55:59 cri

Annobar cutar Ebola a yammacin Afrika za ta janyo raguwar GDP daga kashi 1 cikin 100 zuwa kashi 1,5 cikin 100 a cikin kasashen shiyyar, in ji shugaban bankin cigaban Afrika (ADB), Donald Kaberuka a ranar Talata a birnin Abidjan.

A yayin wani bikin sanya hannu kan ba da taimako tare da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, mista Donald Kaberuka ya bayyana cewa, cutar Ebola ta kasance babbar barazana ga rayuka, da kuma ayyukan kiwon lafiya, haka ma barazana ce ga tattalin arziki ga kasashen yammacin Afrika da wannan cuta ta fi shafa.

A cikin hasashenmu na farko, raguwa daga kashi 1 cikin 100 zuwa kashi 1,5 cikin 100 ba za ta kasance abu mai wuya ba cikin wannan hali, in ji wannan jami'i.

A cewar Kaberuka, a cikin wadannan kasashen wato Guinee, Liberiya da Sierre Leone, da suka soma farfadowa daga rikicin soja da na siyasa, annobar Ebola na kawo babbar barazana ga ayyukan noma, lamarin da zai iyar haifar da matsalar abinci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China