in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta gayyaci masu gaba da juna a Sudan ta kudu zuwa tattaunawar sulhu
2014-02-06 16:20:43 cri
Kungiyar huldar gwamnatocin kasashen gabashin Afrika da ci gabansu IGAD a ranar Laraban nan ta sanar da cewa ta gayyaci bangarori masu fada da junansu a kasar Sudan ta kudu domin wani zagayen tattaunawar sulhu da za'a yi a ranar 10 ga watan Fabrairun da muke ciki a kasar Habasha.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a Nairobi, manzannin wannan kungiyar dake kula da kasashen yankin gabashin Afrika wadanda suka rigaya suka tattauna da Shugabannin kasashen Kenya da Habasha sun kuma gayyaci fursunonin siyasa da aka saki makon da ya gabata da su halarci tattaunawar.

Sanarwar ta yi bayanin cewa a lokacin zaman tattaunawa da mazannin kungiyar suka yi a biranen Adis Ababa da Nairobi, sun fitar da tsarinsu tare da bukatar Shugabannin kasashen da su lura da ayyukan da suke yi kafin zaman tattaunawa zagaye na biyu da zai maida hankali a kan tattaunawar siyasa da kuma sulhuntawa a kasar baki daya.

Manzannin na musamman sun bayyana cewa za'a tura masu lura da tantancewa ne a shiyyoyi daban daban a kasar Sudan ta kudu sakamakon rahoton da kwamitin hadin gwiwwa ya samar.

Wannan tattaunawar sulhun da kungiyar ta IGAD ta dauki nauyi an fara shi ne a watan Janairun, inda masu shiga tsakani suka ce sai bangarorin duka biyu sun dauki matakai da dama yanzu da suka rigaya rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Haka kuma manzannin sun ce bangarorin biyu sun jaddada cewa tashin hankali da yaki ba su ne kuma ba za su zama mafita ga matsalolin da ake fuskanta ba a kasar ta Sudan ta kudu, don haka a shirye suke su tattauna su kuma yi aiki tare domin ganin an yi tattaunawar siyasa don sulhu a kasar baki daya da kawo karshen tashin hankalin. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China