Philip Aguer kakakin Sojin yace sojojin gwamnati bayan wannan nasarar na kwato duk garuruwan dake da arzikin man fetur a kasar yanzu haka tana kokarin ganin ta kwato garin Bor.
Anyi bata kashi sosai tsakanin bangarorin Machar dana Gwamnatin amma na gwamnati sunyi nasasa akan 'yan adawa inji Philip wanda baiyi wani bayani ba bayan hakan.
Garin Bantio yana da muhimmanci sosai a matsayin babban birnin jihar Unity wanda rijiyoyin man sa yake samar da ganga 45,000 a duk rana. (Fatimah Jibril)