A cikin sanarwar, Ban ya yi murnar nasarar cimma yarjejeniyar a karkashin sulhuntawar da kungiyar IGAD ta yi. Yanzu akwai bukatar a ci gaba da yin shawarwarin siyasa da zai kunshi wakilan 'yan siyasa da na sassa masu zaman kansu na kasar, da nufin cimma wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a dukkan fannoni.
Ban da wannan kuma, Ban ya ce, MDD za ta kara kokarin da take yi na kiyaye fararen hula dake fuskantar hadari, da ba su taimakon jin kai da suka wajaba. Har illa yau dai, Ban ya kara yin kira ga sassa daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su tabbatar da 'yancin tawagar musamman ta MDD dake kasar wato UNMISS, da ma'aikata masu aikin jin kai, da masu sa ido kan hakkin bil Adama wajen gudanar da ayyukansu a kasar. Kana kuma Ban ya yi yabawa da gwamnatin kasar Sudan ta Kudu saboda goyon bayan da ta baiwa UNMISS. (Bilkisu)