Kafin haka, karkashin shiga tsakani daga IGAD, gwamnatin Sudan ta kudu da wakilan 'yan adawa sun daddale wannan yarjejeniya a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. Game da wannan batu, Qin Gang a jawabin da ya yi ma manema labaru yayi fatan bangarorin biyu na kasar Sudan ta kudu za su tabbatar da daina bude wuta ba tare da bata lokaci ba, tare kuma da shimfida wani yanayi mai kyau wajen daidaita wasu matsaloli.
Bugu da kari, Mr Qin ya jadadda cewa, Sin na amincewa da kokarin da IGAD ta yi, kuma don daidaita rikicin kasar Sudan ta Kudu, Sin ta yi kokarin tuntubar bangarori daban-daban, gami da kokarin shiga tsakaninsu. A nan gaba, Sin za ta ci gaba da hadin kai da bangarori daban-daban ciki hadda IGAD ta yadda za a sa kaimi ga samun zaman lafiyar da kwanciyar hankali a kasar ta Sudan ta kudu. (Amina)