Dadin dadawa, sanarwar ta ce, ya kamata a kiyaye tsaron manema labaru a wasu wuraren da ake fuskantar rikice-rikice da daidai da fararen hula bisa dokar jin kai ta kasa da kasa. Kwamitin ya nemi bangarorin daban-daban dake gaba da juna dasu dauki alhakin dake wuyansu na kiyaye fararen hula.
Sanarwar ta nemi wannan kungiya da ta saki dukkan mutanen da take tsare da su ba tare da wani sharadi ba. Kwamitin kuma ya jaddada niyyarsa na gurfanar da masu aikata irin wannan laifin na ayyukan ta'addanci a gaban kotu.
Wani jami'in dake ba da taimako ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasar mista Ben Rhodes ya bayyana a ran 22 ga wata cewa, ba shakka yadda kungiyar ISIS ta kashe wannan dan jarida hari ne ga kasar Amurka. Kuma kungiyar ta riga ta kashe duban fararen hula, kuma hakan babbar barazana ce ga kasashen duniya, domin haka ne Amurka take kokarin sa ido kan ayyukan kungiyar domin ganin ko za ta yi shirin kai hari a kasashen yammacin duniya ko a'a. (Amina)