in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka a zagaye na 6
2014-07-01 10:42:52 cri
Ma'aikatar harkokin waje da ma'aikatar kudi ta kasar Amurka sun sanar da shirin gudanar da shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka zagaye na 6, shawarwarin da za a yi tun daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Yuli a nan birnin Beijing na kasar Sin.

Bangaren kasar Amurka ya ce, manzon musamman na shugaban kasar Barack Obama kuma sakataren harkokin wajen kasar John Kerry da ministan kudi na kasar Jacob Lew tare da manzon musamman na shugaban Sin Xi Jinping kuma mataimakin firaministan kasar Wang Yang da memban majalisar gudanarwar Yang Jiechi za su shugabanci shawarwarin. Ana dai sa ran maida hankali kan kalubale da dama da kasashen biyu za su fuskanta a fannin moriyar da za a samu daga tattalin arziki da manyan tsare-tsare a tsakanin su, da yankuna su, da ma fadin duniya baki daya.

A baya ma dai, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka mai kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasific Daniel Russel ya bayyana cewa, Amurka da Sin za su yi musayar ra'ayoyi kan halin da kasashen Sudan, Afghanistan, Iran, Koriya ta Arewa, Ukraine, Iraki ke ciki, da kuma batun ikon mallakar tekun gabas da tekun kudu. Kana za su tattauna kan yadda za su yi hadin gwiwa don sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya. Haka nan kasashen biyu za su yi kokari tare wajen tinkarar sauyin yanayi, da kara hadin gwiwa a fannin samar da makamashi mai tsabta, da kuma tattauna kalubalen da suke fuskanta a fannonin yaki da ta'addanci, fasa-kwaurin namun daji da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China